Cikakken Tarihin Bash Ne pha
Suna: Bashir Halliru Alhassan
Inkiya: Bash Ne Pha
Kwarewa: Waka
Shekaru: 1998
Gari: Jos
Kasa: Nigeria

WANENE BASH NE PHA
Bashir halliru Alhassan Sananne kuma Fitaccen mawakin arewacin Nigeria na salon Hausa rap Wadda akafi sanida “Bash Ne Pha” na daya daga cikin mawakan rap dake tashe Kuma suka samu karbuwa lokaci guda.
HAIHUWARSA
An haifeshi a garin jos, plateau dake nigera a Shekarar alib dubu daya da dari Tara da casa’in da takwas (1998).
karanta: Cikakken Tarihin Abdullahi Andaz
KARATU
Acikin garin jos plateau Kuma mawakin yayi Karatunsa na primary da secondary Wadda bayan kammala karatunsa yafara aikin gyaran mota wato kaninakci kafin yafara Waka.
FARAWA
Bash yafara Waka ne da wakarsa ta “Yar’alaji’ dakuma Wakar ‘Jos” Shekarar dubu-biyu da sha-tawaks 2018, Alokaci daya yasamu karbuwa da wakarsa tafarko a wajen masu sauraron wakokin Hausa.
Ganin hazakar mawakinne yasa FKG Entertainment sukayi signing dinsa da record level dinsu.
Bash Neh Pha Nau’in kida dakuma Salon wakarsa Na Musamman ne.
Yawancin Maudu’in Kiɗansa yana mai da hankali kan batun Gaskiya, da Salon Sa Ya Kunshi Kalma, Nishaɗi tare da Darasi.
Acewarsa ganin Yadda Mahaifiyarsa Ke Kula Da Shi Da Son Sa, Daga Nan Ya Fara So. Ku Fara Yi Mata Waka.

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN ALI ARTWORK
Bash Neh Pha Yayi Wasan Tare Da Side Many Top Arewa & Nigerian Artists, Kuma Wakar Sa Na Kwanan Nan Da B.O.C Madaki “Bullet” Ya Sa Jama’a Da Yawa Su Mika wuya Ga Iyakar Bajinta.
An yi hira da shi a gidan talabijin na Arewa24, kuma faifan Bidiyon da ya saba yin su a gidajen Talabijin da dama a Afirka. Haka kuma wakokin sa na Audio dake Wasa a duk gidajen Rediyon Jihar Arewa. Gudanarwar Sa Suna Kula da Shi Na Kyau, Da Kuma Inganta Shi Da Kyau.
DAUKAKA
Bash yasamu daukaka sosai Ganin yadda akalarsa ta sauya lokaci guda, Izuwa yanzu ana lissafata shi cikin taurarin mawakan Hausa rap na arewacin Nigeria sannan yayi wakoki dadama da manyan mawaka irinsu Adam A Zango, Boc dasauransu
Kawo yanzu 2022 bash yayi wakoki samada Ashirin 20, sannan yabada tarun magoya baya a shafinsa na YouTube na samada 9.8k subscribers
JERIN WAKOKIN BASH
Jerin wakokin Bash sun hadada
Mama
Saina Fada
Yar Alaji
Amisali
Matsalar arewa 2021
Bullet ft Boc madaki 2021
Inaso ki sanni 2022
Up9ja 2022
Ashekarannan 2022
Ramadan 2022
Domin Karin bayani dangane da Cikakken Tarihin Bash Ne pha kokuma wasu jaruman kuziyarci YouTube namu Nw Hausa TV.