Tarihin falalu a dorayi
SUNA: falalu a Dorayi
CIKAKKEN SUNA: falalu abubakra Dorayi
SHEKARU: 1977
AIKI: director, jarumi kuma producer,
AURE: yanada aure
MATAKIN KARATU:
Difloma
GARE: kano
KASA: Nijeriya
WANENE FALALU A DORAYI
Abubakar Dorayi wadda akafi sani da falalu a dorayi yakasance shahararren me shirya film kuma mai bada umarni a masana’antar kannywood wadda yayi fice cikin kasar dakuma nahiyar Africa gabadaya.
Falalu a dorayi shine mashiryi kuma jarumi a cikin shirin dogon Zango wadda ake sakewa a tashar Arewa24, Mai suna
“gidan badamasi”
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN HAFSAT IDRISS
HAIHUWARSA
An haife shi a ranar hudu ga wata janairu a shekarar 1977) cikin garin Dorayi gwale dake jihar kano. Mahaifinsa alhaji abubakar yakasance Dan kasuwa ne a garin kano.
KARATU
Yayi makarantar firamare da sakandare a jihar kano, yakuma sami difloma a fannin sadarwa daga jami’ar bayero dake kano sannan ya samu difloma a harkar shirya fim da talabijin a jami’ar maitama sule da ke kano a shekarar ta 2017.
Yasake halartar shirin horar da fim a kwalejin asiya ta fim & amp talabijin noida dake kasar indiya.

KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN HAMISU BREAKER
FARA SHIRI A KANNYWOOD:
falalu a dorayi ya fara hakar fim ne a shekara ta Alib 1997, tare da wata kungiyar wasan kwaikwayo a lokacin da yake makarantar sakandare bayanya kammala karatunsa na sakandare a Dorayi ya shiga masana’antar shirya fina finai ta kannyood.
Ya samu damar aiki tare da sarauniya films inda ya shirya fim mai suna “kwangiri”, sannan” uwargida dakuma majalisa.
SAMUN DAUKAKA
Duk da dadewarsa a masana’antar shirya fina finan Hausa Dorayi ya yi ficene a fim din dayayiwa Jarumi Adam a Zango daya bada umarni Mai suna basaja.
Yasha yiwa manya Kuma fitattun yan wasa da suka hada da ali nuhu, da adam a zango, da Hadiza Aliyu fim Wadda Kuma sun samu karbuwa a ciki Dama wajen masana’antar kannywood.
Sannan 2015, falalu a Dorayi ya shirya” wani fim mai suna gwaska, Wanda jarumi Adam a zango ya bayar da umarnin, daga bisani yasake fitar da “Return of gwaska a shekarar ta (2017).
Tin daga shekarar 2019 zuwa 2022, falalu a Dorayi ya jagoranci kuma ya taka rawa a shirinsa mai dogon Zango da ake sakewa a manhajar arewa24 mai suna
“gidan badamasi” Wanda ake sabuntashi duk shekara inda yafito a matsayin maigadi a cikin shirin( Taska).
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN HAMISU BREAKER
JERIN FINA FINANSA
-Bana bakwai.2007
-Artabu.2009
-Ahlul kitabi.2011
-Sandar kiwo.2011
-Sayyada.2011
-Andamali.2013
-Mai dalilin aure. 2014
-Soyayya da shakuwa 2014
-Akwai hanya.2016
-Gwaska.2017
-Juyin sarauta.2017
-Alkibila.2018
-Allo
-Farar saka
-Fataken dare
-Fitilar dare
-Ibro Dan Fulani
-Larai
-Madugu
-Mukaddari
-Namamajo
-Ragas
-Sa’a dai
-Sowa
-Tarkon kauna
-Tasrtuwa
-Yau a gari
-Zatona
-Zo mu zauna
-makahon daji
-Shaheeda
-Kwana chasa,in shiri mai dogon zango wadda ake haskawa a Arewa24
-Gidan badamasi 2019
-Gidan badamasi 2020
-Gidan badamasi 2021
Kalli videon Nan Domin Karin bayani danganeda Tarihin falalu a dorayi a YouTube Nw Hausa Tv
Kuyi SUBSCRIBE