Cikakken tarihin Hamisu breaker
SUNA: Hamisu sa’id Yusuf,
Hamisu Breaker
SHEKARU : 1992
MATA : baida mata
AIKI: Mawaki,
Jarumi
JIHA: Dorayi, KANO
KASA: Nigeria

WANENE HAMISU BREAKER
Hamisu yakasance Mawakin hausa kuma jarumi Wanda yayi fice a fadin Nigeria musamman arewa dama nahiyar Africa gaba daya.
cikakken sunansa Hamisu Sa’id yusuf Amma anfisaninsa da hamisu breaker
Ya samu suna breaker ne tin yana dan rawa sabida irin kwarewarsa ake kiransa da breaker.
HAIHUWAR HAMISU BREAKER
Mawakin Ya kasance haifeffen garin Kano an haifeshi a 1992 a dorayi karamar hukumar kwale.
KARATUNSA
Mawakin yayi Primary da Secondary a dorayi amma haryanzu bai samu damar cigaba da karatuba.
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN FALALU A DORAYI
DAUKAKAR HAMISU BREAKER
Breaker ya fara Waka tun yana makarantar islamiya yayi wakoki da dama kafin ya fara cire albums.
Mawakin yayi wasu finafinain kannywood kamarsu zainul abideel, sannan kuma yana hawa videon wakokinsa dakansa duk dacewa yakan baiwa Sauran jaruma kamarsu Kb international, Garzali miko, Mome Gombe dasauransu suhau wakar tasa.
Taurarinsa Sun fara haskawa a 2016 tinda ya fitar da wakar shimfidar fuska
Sannan ya Kara samun shahara da magoya baya tun bayan fidda Wakarsa ta jarumar mata Dayayi a shakarar 2020.
Wakarsa ta jarumar mata tasamu karbuwa inda mutane sama da million suka kalleta. Wakar ta kasance tana daga cikin jerin wakokin da sukafi shahara cikin wakokin hausa.
HADAKA
Mawakin yayi waka tareda mawakanda suka hada da Isah ayagi, namej, faruk m inuwa, lilin baba, Abdul katif dasauransu

KARRAMAWA
Wakar Jarumar Mata da ta ja hankali a arewacin Najeriya ta samu shiga fagen nazari a Jami’a, inda mashahurin malamin nazarin adabin baka Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau yayi dogon Bincike dakuma nazari kan yadda wakar tasamu karbuwa wajen al’umma.
Turntable chart ta wallafa cikin jerin wakokin tana tantance wadanda suka fi shahara a YouTube inda ta hamisu breaker tazo na shida a wancan lokacin.
Kuma Hamisu yayiwa masoyansa alkawarin fidda wakar jarumin maza.
Sannan a 01/02/2022 Charts Africa ta zayyana wakarsa mesuna Dan dako a masayin bidiyon waka na bakwai da akafi kallo a manhajar youtube a Nigeria.
MATAR HAMISU BREAKER
Kawo yanzu Mawakin baida mata kuma babu sahihin labarin wata budurwa da aka alakantasu ta shi
ALBUMS
Mawakin yasake albums da dama da suka hada da :
-Haseena
-Dalilin so da
-Sone
-Sakon amarya
-Sirrin zuciya
-Kalmar so
– Bangaji ba dasauransu
WAKOKIN HAMISU BREAKER
Sannan daga cikin albums nasa akwai wakoki dasu shahara sosai kamarsu
-Jaruma 2020
-Bangajiba 2021
-Sai dake 2021
-hasina
-zumar kauna
-Kanwata 2021
-Sone
-Yadda kunne yaji
-So 2022
-Shimfidar fuska
-So gaskiya ne 2022
-Dan dako 2022
BIDIYON WAKOKI
Kuma yafito a bidiyoyi wakoki da dama kamarsu
-Dan dako 2022, wanda yafito tare da *Ado gwanja *tynkingmaigsahi *Aisha najamu wadda akafi sani da nafisat izzar-so
Dadai sauransu
-So gaskiya ne 2022 wanda yafito tare jarumai mata da yawa kamarsu *Amal umar *Maryam booth *Nana izzar-so dadai sauransu
-Daga yarda wadda yafito tare da *momee gombe
-Karshen kauna tareda *rakiya musa
MABIYA
Yanada nadaga cikin mawaka dasukeda dubbunan mawaka a shafukansa na sada zumunta inda yakeda mabiya samada million a Instagram.
Sannan yakasance daya daga cikin ambassadors na YBN Yahaya bello network
Karanta: CIKAKKEN TARIHIN YUSUF SASEEN
Kalli wannan videon Domin Karin bayani dangane da cikakken tarihin hamisu breaker a YouTube Nw Hausa Tv