Cikakken tarihin Nura m inuwa
SUNA: Nura m inuwa kokuma M inuwa
HAIHUWA: 18 September 1989
MATA: [1] Amina tin shekarar 2017
YARA: [1] Farra m inuwa
AIKI: marubucin waka,Waka, producing,
Kasuwanci
JIHA: KANO
KASA: Nigeria

WANENE NURA M INUWA
Nura m inuwa Wanda akafi sani da nura, ko kuma m inuwa Shahararren mawaki a arewacin Nigeria Wanda yayi fice a duka nahiyar Africa. Mawakin yana daya daga cikin manyan mawakan harshen hausa wadanda kuma suka samu daukaka da tarun lambobin yabo.
HAIHUWARSA
Anhaifi nura m inuwa
A shekarar 1989 18 September a garin Kano, cikin gwammaja, karamar hukumar Dala,
KARATUNSA
mawakin yayi karatunsa daga primary zuwa secondary a kano cikin garin gwammaja, sannan ya kasance mawakin Hausa kuma producer a masana,antar kannywood
Karanta CIKAKKEN TARIHIN HAMISU BREAKER
DAUKAKAR NURA M INUWA
Ya fara waka a shekarar 2007 ya fara ne da wakar siyasa amma nasararsa tafara ne daga shekarar 2010. Mawakin nayin salon wakokin siyasa, aure, zauranci, soyayya da kuma wakokin finafinan shirin kannywood.
Wasu wadanda ba asan ko suwayeba Sun wasa masa ruwan acid a shekarar 2012
Nura yayi waka tare mawaka dayawa kamarsu Umar m sharrif, Billi’o, Ali show dade sauransu sanan a wakarsu ta siyasa a shekarar 2015 yayi hadaka da mawakan siyasa na arewa Irinsu Rara, Aminu ala, hussaini danko, Adam a Zango, Ali jita, Nazifi Asnanik, Dade sauransu. Kawo yanzu mawakin Yayi wakoki da suka Kai 550 wacce yafiso itace rigar aro
WAKOKINSA
Wakokinsa Sun hada da
-Aisha humaira
-rigar aro
-mai zamani
-ango
-bansanwani sarkiba
-Aisha humaira
-zurfin ciki
-alkuki
-soyayyar fesbuk
ALBUMS
Sannan yayi albums dadama kamar su
-makashinka 2012
-afra 2015
-rigar aro 2015
-soyayya 2016
-siyan Baki 2017
-matan gida 2017
-wasika 2018
-manyan mata 2018
-ranar aurena 2018
-dan magori 2018
-mai zamani 2019
-ango 2019
Sannan yayi alkawarin cire albums a 2021
-ni da ku,
-lokaci
DANGANTAKARSA DA ABOKAN AIKINSA
Babban abokin nura a kannywood shine Abdul Amart wadda sukayi hadaka wajen bude kamfaninsu na shirya fina finai mesuna Abnur entertainment. kamfaninsu ya shirya finafinai kamar su Afra, Rigar aro, Salma, da dai sauransu.
Sannan akwai wakarsa da yake cewa Adam A Zango garkuwatace hakan nanuna yadda Zango keda muhimmanci a wajen mawakin. Yakuma kara dacewa Mu’azzam idi yari yayane awajensa.
Kawo yanzu mawaki Nura yana da mata daya Amina wadda ya aureta a shekarar 2017 yana kuma da Yarinya dayamesuna
Farra

Karanta CIKAKKEN TARIHIN LAWAN AHMED
KARIN BAYANI
Daga bangare daya kuma Nura bayan waka, shirya finafinai dakuma rubuta waka dayakeyi yakasance cikakken dan kasuwa ne shi.
Mawakin hausa na farko da masoyansa sukayimasa
Zanga zanga akan ya cire musu album
A shekarar 12 February 2021
Babban yaronsa a bangaren waka
Shine -saniyo m inuwa, sauran yaransa kuma su Ali show, faruk m inuwa dadai sauransu
Sannan yasha karbar Award daga kungiyoyi da dama a fadin duniya da kyautar girmamawa
Babban burinsa arayuwa yaga ya birge masoyansa.
YABO DA KARRAMAWA
Abinda ali nuhu yace akansa
Alinuhu yace betaba ganin mawaki me basira kamarsaba
Shikuma aminu ala cewa yayi betaba ganin mawaki me yalwar harshe kamar nura m inuwa bah
Umar m Sharif kuma cewa yayi nura mawakine da de iyayin Waka akowana irin yanayi kuma akowana fanni
Nura mawakine da yasha karbar yabo daga masoya da abokanan aiki da kungiyoyi saboda kwarewarsa afannin waka da mu amalarsa da mutane.
Nura yasamu karbuwa a shafukan na YouTube, Instagram, twitter dakuma Facebook.
Mawakin Nada mabiya a Instagram samada 1.5 million a 2022
Domin Karin bayani
Dangane da cikakken tarihin nura m inuwa
a YouTube Nw Hausa Tv