Cikakken tarihin Ramadan booth
SUNA: Ramadan ado Muhammed
INKIYA: Ramadan booth
SHEKARU: 7 may 1989
AIKI: Jarumin fim, darakta, furodusa,dan kasuwa
MATA: Daya
YARA: 1 Yarinya Mace
GARI: Kano
KASA: Nigeria

WANENE RAMADAN BOOTH
Shahararren matashin jarumi a masana,antar shirya fina-finan hausa na kannywood Ramadan ado Muhammed wadda akafi Sani da Ramadan booth ya kasance daya daga cikin matasan jaruman da tauraronsu suka haska a baya kuma suke cigaba da haskawa a yanzu.
Jarumin ya fara fitowa a fina-finan hausa ne tun yana da kananun shekaru
HAIHUWARSA
Jarumin Ramadan booth anhaifeshine a shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da tara a ranar bakwai ga watan biyar 1989-7-5 a cikin garin kano dake Nigeria mahaifinsa yakasance bature ne dan kasar Scotland.
KARANTA: Tarihin Rabi’u Rikadawa (Baba Dan Audu)
KARATUNSA
Yayi karatunsa na primary a ebony nursery and primary school sannan yayi secondary nasa a makarantar mahammadiyya secondary school a garin kano.
IYALI
Kana yana da mata daya fatima da yarinya daya
Sannan yana da yan’uwa da yawa wadda suma sun kasance jarumai a masana,antar ta shirya fina-finan hausa
Kamarsu
| jaruma maryam booth (Yar’uwa)
| jarumi amude booth (Kani)
| jaruma zainab booth wadda takasance mahaifiya ce a gareshi asalin bafulatana yar Nigeria.
DAUKAKARSA
Jarumin ya dade a masana’antar Amma taurarinsa sun fara haskawa ne a Shirinsa dayayi maisuna Ashabul kahfi Shirin da yayi atareda jaruma irinsu Nuhu Abdullahi Sadeeq sani Sadeeq dadai sauransu.
Shirin da Jarumi Ali Nuhu yayi Masa Mai suna “Gamunan dai ” takara haskawa jarumin taurarinsa yakuma Kara sanuwa dakuma Taryn madoya
JERIN FINA-FINAI
Booth ya fito a fina-finai da dama kamarsu
•ashabul kahfi
•gamu nan dai
•auren jeka nayika
•talaka bawan Allah
•bana bakwai
•ga da ga
•wutar kara yaki a soyayya
•jani muje
•gwarzon shekara
•safeena
•sadaka yallah
•izzatu
•so da so
•matar muce
•sanam
Da dai sauransu
HADAKA
Sannan yafito tare da jaruman masana,antar shirya fina finan na hausa da dama
Kamarsu
*Ali nuhu
*Shamsu dan,iya
*Maryam booth
*Marigayiya Zainab booth
*Nuhu abdullahi
*Abdul m shareef
*Garzali miko
*Jamila nagudu
*Baballe hayatu
Da dai sauransu
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN DADDY HIKIMA
KYAUTAR GIRMAMAWA
Kana yasha karbar kyautukan girmamawa da dama
Kamarsu
_inside business African commendation award (best young upcoming actor 2017)
_African alive film award wadda akabasu a London tare da jaruma nafisa abdullahi
_Kannywood award (young upcoming actor 2018)
_sautin arewa entertainment award
(Most impressive actor 2019)
Da dai sauransu
Zaku iya ziyartarmu a shafinmu Na YouTube mesuna NW HAUSA TV domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin ramadan booth